Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Fatima (a.s) Ma'abociyar Hijira

Fatima ta shaida lokacin kace-na-ce din da'awa a Makka a lokacin tana yarinya karama. Ta rayu cikin wahalhalun mahaifinta (s.a.w.a) da abin da ya same shi da musulmin farko na kuntatawa da cutarwa. Mushrikan Makka dai sun nuna kiyayya da cutar-warsu ga Manzon Allah (s.a.w.a), kuma Annabi ya jure duk wannan saboda Allah, Fatima ma ta yi tarayya da babanta a jarrabawa da hakurinsa a lokacin tana karama.

Daga irin wannan cutarwa ne wata rana wani daga cikin kafirai ya jefa turbaya a fuskar Manzon Allah (s.a.w.a) da kansa, Manzo ya jure wannan ya tafi gida yana mai hakuri, alhali turbayar ta bata fuskarsa da kansa, sai Fatima -tana karama- ta ga babanta a irin wannan hali, nan take ta tafi ta kakkabe masa, ta debo ruwa don ta wanke masa kansa da fuskarsa, (a lokacin) sai hankalinta ya tashi, bakin ciki ya rufe ta, sai ta shiga kuka. Wannan ya yi Manzon Allah (s.a.w.a) tasiri, don haka ya yi ta kokarin lallashinta yana shafa kanta a hankali tare da tausayawa yana ce mata:

"Bar kuka 'yata, domin Allah ne mai kare babanki kuma taimaka masa a kan makiya addini da sakonsa(1)".

Cutarwar Kuraishawa ba ta tsaya a nan ba, sai dada fadada take yi, kafirai sun ba da dukkan iyawarsu wajen ganin bayan Manzon Allah (s.a.w.a) ta hanyar kashe shi, bayan sun yanke kauna daga danne sautinsa da dushe hasken kiransa. Don haka Manzo (s.a.w.a) ya kuduri yin hijira zuwa Yathrib (Madina).

Manzon Allah (s.a.w.a) ya fita daga Makka a boye cikin dare, ya bar garin haihuwarsa da masoyansa da iyalinsa, daga ciki har da Fatima 'yarsa kuma abin sonsa, da dan Baffansa Ali bin Abi Dalib (a.s.), mai taimakonsa, abin dogararsa kuma takobinsa mai sara. Inda bar Ali kwance a bisa shimfidarsa, da kuma masa wasicin da ya mayar da amononin da suka kasance a hannunsa (Annabi) zuwa ga masu su; sannan ya hore shi da ya same shi (daga baya) tare da iyalinsa.

Sai Ali ya aiwatar da wasicin, ya sayi ababen hawa don daukar mata, ya hada iyalinsa, tare da Fadimomin Bani Hashim, wato: Fatima al-Zahra 'yar Annabi (s.a.w.a), da Fatima bint Asad, mahaifiyar Imam Ali (a.s.) kuma wadda ta reni Annabi (s.a.w.a), da Fatima 'yar Zubairu dan Abdulmudallib da Fatima 'yar Hamza dan Abdulmudallibi (biyun karshen nan) 'ya'yan baffan Annabi (s.a.w.a) ne.

Sai ayarin Ali (a.s.) ya kama hanyar zuwa haduwa da Manzon Allah, Manzo (s.a.w.a) kuwa da ma ya isa Yathrib, ya sauka a Kubah(2)",ya tsaya a nan yana jiran isowar Ali da Fatima. Ya kasance yana cewa wadanda ke tare da shi na daga wadanda suka bukace shi da ya shiga Yathrib, cewa:

"Ba zan shige shi ba har sai dan baffana da 'yata sun iso (3)

Ali (a.s.) ya ci gaba da tafiya a kafa ba tare da ya hau abin hawa ko ya yi amfani da wata dabba ba. Haka ya share tsakanin Makka da Madina a kafa, har sai da kafafunsa suka kumbura saboda tsananin tafiya.

Yayin da ayarin ya iso Kubah Manzo (s.a.w.a) ya yi matukar farin ciki saboda isowarsu lafiya da haduwa da masoya, ya ce: "Ku kira min Ali" sai aka ce ai ba zai iya tafiya ba. Sai Manzo ya je wajensa ya rungume shi ya zubar da hawaye saboda tausayawa halin da kafafunsa suka shiga, sannan sai ya yi addu'a ya tofa a kafafun, daga nan bai kara jin ciwonsu ba har ya bar duniya(4).




____________
1- Al-Husaini, Siratul-Mustafa, bugu na uku, shafi na 205.

2- Kubah wani dan gari ne dake kimanin mil biyu daga Madina a kan hanyar zuwa Makka. A nan ne aka fara assasa masallacin farko a Musulunci. Hadisai da dama sun yi bayanin darajojin wannan masallaci.

3- Al-Husaini, Siratul-Mustafa, shafi na 258.

4- Siratul-Mustafa, bugu na 3, shafi na 258.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


80s toys - Atari. I still have